HOTUNA: Yadda ‘yan Argentina suka yi murna bayan dawowar su gida da kofin duniya

0
97

An yiwa ‘yan wasan kasar Argentina da suka lashe gasar cin kofin duniya a birnin Buenos Aires da sanyin safiyar Talata.

Bayan an tashi wasan cin nasara a Qatar, tawagar karkashin jagorancin kyaftin Lionel Messi sun samu tarba da dimbin jama’a wadanda suka yi jerin gwano a kan tituna cikin murna da dawowar jaruman nasu.

Messi ne ya fara sauka daga cikin jirgin yayin da yake rike da kofin zinare a sama domin ganin jama’a.

Daga nan ne aka nada jan kafet domin sanya tawagar masu nasara yin tafiya yayin da ‘yan jarida da jami’ai da ’yan kungiyar suka tarbe su.

Daga nan kuma suka tashi daga filin jirgin, suna tafiya a kan wata budaddiyar motar bos zuwa hedikwatar hukumar kwallon kafa tasu.

An shirya babban bikin ne a wurin tunawa da Obelisk babban birnin kasar da tsakar rana (15:00 GMT) ranar Talata.

Gwamnatin Argentina ta ce ranar za ta kasance ranar hutu ta banki domin magoya baya “su iya bayyana matukar farin cikin su ga tawagar kasar”