Gabatarwa
A wannan karon ma Hausa24 tazo muku da tarihin fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’antar Kannywood Ado Isah wanda kukafi sani da (Gwanja) tun daga shekarunsa na kuruciya har izuwa shigar sa masana’antar Kannywood.
Wanene Ado Isah (Gwanja)
Ado Isah Gwanja an haife shi 22 ga Janairu 1990 mawakin Najeriya ne kuma jarumi a masana’antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood.Â
Gwanja dai ya fara fitowa a fina-finai ne a shekarar 2017, amma ya dauki tsawon lokaci a harkar waka kafin ya fara wasan kwaikwayo. Gwanja sau da yawa an fi saninsa a waka fiye da a fim, gwanja ya kware a wakokinsa na mata, ana gayyatarsa ​​zuwa bukukuwa inda yake rera wakokinsa, gwanja ya nada tsohon mawakin Hausa Aminu Mai Dawayya a matsayin jagoransa.
Wasu daga cikin fitattun wakokin Gwanja akwai Kujerar Tsakar Gida, Mamar-Mamar, ÆŠakin Ba ciwonwa, Asha Rawa-rawa, Kilu ta Ja Bau, Kidan Mata, Warr da Chass da sauransu.
Kundin wakokin sa
Wadannan sune jerin kundayen wakokin sa
-
Suna                     Shekara
-
Kujerar Tsakar Gida.       2014
-
Indonesia                 2017
-
Matan Arewa              2016
-
Yuli                       2018
-
Ga Gwanja                2017
-
Tangaran                  2021
-
Adama                    2021
Kyaututtukan daya samu
Gwanja ya samu kyaututtuka da dama daga daidaikun mutane da kungiyoyi, daga cikin manyan lambobin yabo da Gwanja ya samu akwai kyautar da uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bayar. Sauran kyaututtukan sun hada da;
-
2019 ya Samu Gwarzon Jarumin Kano.
-
2018Â ya lashe kyautar Sani Abacha Youth Center ta gwarzon dan wasa.
-
2018 Kungiyar Dalibai ta kasa (NANS) ta bashi kyautar gwarzon mawakan mata.
-
2019 kamfanin nishadi na(RS) sun bashi kyutar Mafi kyawun Mawaƙi na shekara b Ya Lashe.
-
2018 yayi nasarar zama babban jarumin na (Rhymes Pillars Crew).
Iyalan sa
Mahaifin Ado Gwanja Bahaushe ne dan Kano kuma mahaifiyarsa ‘yar kabilar Shuwa Arabia ce daga jihar Borno, gwanja musulmi ne, ya yi aure da diya daya.
Karshen tarihin Ado Isah (Gwanja)
Anan ne muka kawo karshe tarihin fitacce jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood kenan ku biyomu a Haua24.ng a wani lokacin domin samu cikakkun labarai game da manyan jarumai na masana’antar ta Kannywood harma.