CBN ya kara tsabar kudin da za a cire zuwa N500,000

0
110

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara yawan tsabar kudin da ’yan Najeriya za su iya cirewa daga N100,000 zuwa Naira 500,000 a mako.

Sanarwar da babban bankin ya fitar a yammacin ranar Laraba ta kuma kara yawan tsabar kudin da kamfanoni za su iya cira a mako daga N500,000 zuwa Naira miliyan biyar.

Ta kara da cewa, “A duk lokacin da aka samu wani kwakkwaran dalilin cire fiye da hakan, za a caji kamfanoni kashi 5 cikin 100 na kudin, daidaikun mutane kuma kashi uku cikin 100.”

Sabuwar dokar takaita cire tsabar kudin dai za ta fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Janairu, 2023.

Sai dai ta ce, “Har yanzu ba za a biyan wani tsabar kudin ya haura Naira dubu 100 da wani ya ba shi ba a kan kanta.”

Wannan dai na zuwa ne baan ce-ce-kucen da aka yi ta yi kan sabuwar dokar ta CBN, wadda a kanta Majalisar Tarayya ke neman ganawa da gwamnan bankin domin a kara yawan kudin.