Makomar ci gaba da zaman Messi a PSG

0
120

Lionel Messi zai yi murnar nasarar lashe gasar cin kofin duniya ta hanyar amincewa da ci gaba da zama a Paris Saint-Germain, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka yi ikirarin a ranar Laraba, yayin da yake kokarin kai kungiyar Faransa gasar cin kofin zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 35, wanda ya jagoranci Argentina ta samu nasara a wasan karshe na gasar cin kofin duniya da Faransa da aka yi a Qatar a karshen makon da ya gabata, zai tsawaita kwantiraginsa a babban birnin Faransa na tsawon kakar wasa guda.

Le Parisian da RMC Sport sun ruwaito cewa Messi zai zauna da shugaban PSG Nasser Al-Khelaifi da sauran manyan jami’an kulob din idan ya dawo bayan hutun gasar cin kofin duniya.

Messi ya koma PSG ne a shekarar 2021 kan kwantiragin kaka biyu bayan ya kwashe tsawon rayuwarsa a Barcelona.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai ya tattara kofunan gasar zakarun Turai hudu a 2006, 2009, 2011 da 2015 a Spain da kuma kambi 10 na La Liga.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ya zaburar da Argentina a bugun fenariti a kan Faransa a wasan karshe na gasar cin kofin duniya bayan an tashi wasan da ci 3-3 har karin karin lokaci.

Messi wanda aka zaba gwarzon gasar ya zura kwallaye biyu a wasan inda abokin wasansa Kylian Mbappe ya ci wa Faransa kwallo uku.