HOTUNA: Daga bikin farautar al’adun Irewha na shekara a Nasarawa

0
177

A yau litinin ne bikin farautar al’adun Irewha karo na 4 ke gudana a unguwar Shafa – Abakpa dake karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.

An tattaro cewa bikin farauta da mutane ke yi duk shekara, ya samo asali ne daga garin Ikaka. An ce daya daga cikin wadanda suka assasa al’ummar, Ikaka, ya kasance babban mafarauci, wanda ya yi suna da basirarsa da bajintarsa wajen farauta. Don haka, an ce ana yi masa laqabi da Ada-Ugbe.