Tsananin sanyi ya kashe sama da mutane 20 a Amurka

0
123

Fiye da Amurkawa 200,000 ne suka wayi gari ba tare da wutar lantarki ba a safiyar ranar Kirsimeti sakamakon guguwar sanyi da ta shafe kwanaki ana tafkawa a wasu jihohin gabashin Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20.

Matsanancin sanyi, dauke da guguwa mai cike da tarihi ya mamaye  jihohin Amurka 48 a wannan makon, abin da ya haifar da cikas ga matafiya da dakatar da zirga-zirgar dubban jirage, inda dubban gidaje ke cike da dusar kankara.

An tabbatar da mutuwar mutane 22 a jihohi takwas, ciki har da akalla mutane bakwai da suka mutu a yammacin New York, inda dusar kankara dauke iska mai tsanani suka mamaye garuruwa.

Shugaban gundumar Mark Poloncarz ya shaida wa manema labarai cewa, “Muna da mutane bakwai da aka tabbatar sun mutu sakamakon guguwar da ta afku a gundumar Erie.

Wasu ma’aurata a Buffalo, wanda ke kan iyaka daga Canada, sun shaidawa AFP cewa tsananin sanyi ba zai basu damar tafiyar tsawon minti 10 ba na ziyartar danginsu a bikin Kirsimeti.