Wasu ‘yan garkuwa da mutane sun kashe ‘yan uwa uku da direban da ya kai musu kudin fansa Naira miliyan 60

0
87

Masu garkuwa da mutane sun kashe ‘yan uwansu guda uku da aka sace da kuma wani direban babur bayan karbar kudin fansa naira miliyan 60 daga hannun mahaifin ‘yan uwan a jihar Taraba.

Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne a wani daji da ke kusa da Garin Dogo a karamar hukumar Lau ta jihar a ranar Lahadi.

An tattaro cewa uku daga cikin wadanda aka kashe din iyayensu daya ne kuma masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su a Garin Dogo, inda suka bukaci a biya su N100m.

An tattaro cewa mahaifin wadannan matasa uku, Alhaji Musa, dillalin shanu ne ya tattauna da masu garkuwan.

Aminiya ta gano cewa masu garkuwa da mutanen sun amince da biyan N60m kudin fansa domin a sako ‘yan uwan uku, sannan kuma an dauki hayar direban babur ne domin ya kai kudin fansa ga wadanda suka sace a wani daji da ke kusa da kauyen.

Sai dai masu garkuwa da mutanen sun kashe su hudu bayan karbar kudin fansa. An tattaro cewa an yi jana’izar wadanda aka kashe a ranar Litinin a kauyen.

A wani lamari makamancin haka, sojoji sun bindige wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a garin Maisamari da ke karamar hukumar Sardauna a jihar a ranar Lahadin da ta gabata.

Wadanda ake zargin suna da hannu a yawancin sace-sacen da ake yi a yankin, sun hadu da Waterloo nasu ne a lokacin da suke kokarin yin garkuwa da wani dillalin shanu a yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.