A shirye nake na shiga tattaunawar kawo karshen yaki a Ukraine – Putin

0
108

Shugaba Vladimir Putin ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa don kawo karshen yakin da aka shafe watanni 10 ana gwabzawa a Ukraine, yayin da ya caccaki kasashen Yamma da ya zarga da kokarin wargaza Rasha.

Kalaman na Putin, da aka watsa a ranar Lahadi, sun zo ne a daidai lokacin da dakarun Rasha ke ci gaba da kai hare-hare a garuruwan Ukraine, ciki har da yankunan Kharkiv da Zaporizhia.

Tuni dai wani babban jami’in gwamnatin Ukraine yayi watsi da kalaman na Putin, wanda a watannin baya Amurka ta bayyana a matsayin maras gaskiya kan ikirarin da yake na cewar a shirye yake ya fara tattaunawar kawo karshen yakin da ake gwabzawa, la’akari da yadda har yanzu sojojin Rasha ke kai hare-hare a sassan Ukraine.

Ranar Lahadin da ta gabata, yayin hirar da aka watsa ta gidan talabijin na Moscow Rossiya 1, Putin ya ce, a shirye yake ya tattauna da duk wanda abin ya shafa game da hanyoyin da za a amince da su,amma hakan ya rage ga Ukraine da kawayenta.

A ranar 24 ga watan Fabarairu shugaba Putin ya ba da umarnin mamaye Ukraine, tare da bayyana manufar kifar da abin da ake kira “gwamnati mai ra’ayin salon mulki irin na Nazi a kasar ta Ukraine.

Yakin dai shi ne mafi muni da yankin Turai ya fuskanta, tun bayan yakin duniya na biyu.