Yadda haɓaka kudaden karatun jami’ar Maiduguri zai iya hana marasa galihu yin makarantar

0
227

Samun ilimi wani hakki ne na asali. Yana da mahimmanci don aiwatar da duk wasu haƙƙoƙin ɗan adam kuma ya kamata ya sameshi cikin araha.

Amma da karuwar kudin koyarwa na Jami’ar Maidugiri a baya-bayan nan da kuma hauhawar farashin kayayyaki, shin ilimi zai yiwu?

A cikin wannan al’amari za mu duba yadda karin kudin makaranta da jami’ar Maiduguri ke yi zai hana dalibai marasa galihu zuwa makaranta.