Frenkie de Jong ya sauya shawara kan Man Utd da Arsenal

0
152

Dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, ya sauya shawara kan Manchester United inda yanzu yake son komawa can a bazara.

Monaco ta sayar wa Chelsea dan bayanta Benoit Badiashile, dan Faransa mai shekara 21.

Ga alama za a yi gwagwarmaya tsakanin Manchester United da Chelsea kan sayen dan bayan Inter Milan da Netherlands Denzel Dumfries.

Matashin dan gaba na gefe naShakhtar Donetsk Mykhailo Mudryk, mai shekara 21, ya cimma yarjejeniyar shekara biyar da Arsenal domin komawa kungiyar ta arewacin London.