Kyautar motar sulke da Kwankwaso yayi min ya taimakamin na tsira daga harin bam – Buhari

0
133

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wata mota mai sulke da aka ba shi ta taimaka masa ya tsira daga harin bam da aka kai mai a Kaduna, a shekarar 2014.

Ya bayyana haka ne a wani shirin fim mai suna ‘Essential Muhammadu Buhari’, wanda aka nuna a ranar Lahadi.

A watan Yulin 2014, ayarin motocin Buhari al’amarin ya shafa bayan wasu bama-bamai da suka afku a yankin Kawo na jihar Kaduna.

Buhari wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a lokacin, ya ce shi ne aka kaiwa harin bam din, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Da yake tsokaci kan lamarin a cikin shirin, Buhari ya ce Rabiu Kwankwaso, wanda shi ne gwamnan Kano a lokacin, ya ba shi kyautar motar da yake ciki a lokacin da fashewar ta faru.

“Kwankwaso mutum ne nagari. Ya ba ni mota kirar Land Rover mai sulke,”

“Ya ce ya kamata in yi amfani da ita domin ya yi imanin gasar da nake yi ta hada da mutanen da za su kawar da ni.

“A hanyar zuwa Kano daga Kaduna, sai ga wata mota kirar motar jeep tana kokarin wuce mu sai ‘yan rakiyata suka hana ta wucewa. Abu na gaba da naji kawai shine tashin bam

“Da na duba, sai na ga mutane sun rabu gida gida. Babu daya daga cikin mu da ya samu rauni a cikin motar. Amma ko ta yaya na ga jini a kaina saboda yawan mutanen da bam din ya kashe a waje.