2023: Na roki Allah ya baiwa Obasanjo tsawon rai dan ya ga mulkin Atiku – Melaye

0
112

Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa, Sanata Dino Melaye, ya mayar da martani kan amincewa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi, inda ya ce ya yi addu’ar Allah ya baiwa dattijon tsawon rai ya shaida Shugabancin Atiku a 2023.

LEADERSHIP ta rawaito cewa tsohon shugaban kasa Obasanjo a ranar sabuwar shekara ya fito fili ya amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP gabanin zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na sabuwar shekara mai taken ” kirana ga daukacin ‘yan Najeriya musamman matasan Najeriya.”

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa babu daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar da ya kasance waliyyi, amma idan aka kwatanta ta fuskar ilimi, da’a da kuma abin da za su iya bayarwa, Obi yana da fifiko a kan wasu.