Suarez ya koma wata Kungiya a Brazil Kyauta

0
143

Dan wasan gaban Uruguay Luis Suarez zai koma kungiyar Gremio ta Seria A ta Brazil a kan kwantiragin shekaru biyu har zuwa karshen shekarar 2024, in ji kungiyar.

Suarez ya yi bankwana da kulob din Nacional na kuruciya a watan Oktoba bayan watanni uku inda ya ci kwallaye takwas a wasanni 16 kuma ya lashe gasar cin kofin Uruguay.

A baya dan wasan mai shekaru 35 ya samu nasara a Turai tare da Ajax Amsterdam da Liverpool da Barcelona da kuma Atletico Madrid.

“Daya daga cikin mafi girma a tarihin Uruguay, Luis Suarez yana zuwa don ci gaba da nasararsa,” in ji Gremio a kan kafofin watsa labarun.

“Babban mai zura qwallo, zakara da yawa, kuma mayaki. Barka da zuwa, Luisito.”

Suarez ya koma Gremio na Porto Alegre bayan ya shafe Kirsimeti a Rosario, Argentina, tare da Lionel Messi.