2023: Irin alkawuran da Kwankwaso ya yi wa ‘yan jihar Delta

0
117

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Laraba ya bukaci al’ummar jihar Delta da su yi wa jam’iyyar NNPP ruwan kuri’u a zaben 2023 mai zuwa.

Kwankwaso ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da ofishin yakin neman zaben Hon. Onochie Anthony Ochie a Ogwashi-Uku, da ke Jihar Delta.

Ya ce jam’iyyar NNPP, jam’iyya ce ta kasa da za ta iya samun nasara a duk fadin Nijeriya.

Kwankwaso ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan takarar jam’iyyar NNPP da su dukufa wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben.

Kwakwaso ya yi alkawarin gina ajujuwa 500 a cikin shekaru uku, tare da mayar da yaran da basu samu damar yin karatu ba zuwa ajujuwa sannan kuma zai samar da dimbin ayyukan yi ga jama’ar Nijeriya.