Muna ta tabka abun kunya saboda rashin Sadio Mane a cikin mu — Liverpool

0
106

Tauraron dan wasan kungiyar Liverpool, Alex Oxlade-Chamberlain ya amince cewa kungiyar har yanzu tana fafutukar kwato kanta daga rayuwa ba tare da tsohon dan wasanta na Senegal ba, Sadio Mane.

 

Ya fadi haka ne biyo bayan kashin da kungiyar ta sha a hannun Brentford a gasar Firimiya a daren ranar Litinin.

 

Dan wasan na Ingila ya kuma yi nadamar cewa kwallon da ya ci ba ta da wani muhimmanci mai karfi a wasan da aka doke su da ci 3-1.

 

Liverpool ta fada hannun Brentford a filin wasa na Gtech Community inda ‘yan wasa Uku suka zura musu kwallaye Uku, ta farko Ibrahima Konate (ya ci gidansa) da Yoane Wissa da kuma Bryan Mbeumo.

 

Oxlade-Chamberlain ya yi imanin cewa Liverpool ta yi asarar rashin Mane wanda ya tafi Bayern Munich a bazarar da ta gabata.http://dailynews24.ng