NCDC na fargabar sake barkewar Covid-19 a Najeriya

0
129

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC a Najeriya, ta ce akwai shirin ko ta kwana da ta yi, yayin da ake fargabar za a sake samu bullar annobar Covid-19 fiye da yanda aka fuskanta a baya.

A wata sanarwa da NCDC ta fitar, ta lura da cewa kasashen China, Amurka, Birtaniya, Afirka ta Kudu da kuma Indiya nau’ikan cutar da aka samu a cikinsu na bazuwa a duniya, don haka akwai bukatar a inganta shirin rigakafin wannan cuta.

Sanarwar ta kara da cewa, sashen da aka ware na agajin gaggawa na kuma sa ido kan sake bullar COVID-19 a kasar China, biyo bayan sassauta manufofin kasar na COVID-19, da karuwar wadanda suka kamu da cutar, da yadda ake karbar baki, hadi da mace-mace a Birtaniya da Amurka cikin makonnin da suka gabata.

NCDC ta ci gaba da cewa tun bayan gano nau’in Omicron a watan Disambar 2021, nau’in (BQ.1/BQ.1.1) ya mamaye Najeriya, amma babu daya daga cikin sabbin nau’ikan da aka gano yanzu a Najeriya da kuma ke yaduwa a wasu wurare.

Ya zuwa ranar 5 ga watan Janairu, bayanai daga NCDC sun nuna cewa an samu jimillar mutane 266,450 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 3,155 a fadin jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya, yayin da mutane 661,019,881 suka kamu da cutar inda 6,692,005 daga cikin su suka mutu sakamakon cutar a duniya, in ji WHO.