Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya kara aure

0
184

A ranar Juma’a ne mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya auri muradin zuciyar sa, Hauwa Adam Abdullahi, wadda aka fi sani da Hajiyayye.

Leadership Hausa ta tattaro cewa daurin auren wanda aka dage sau da dama a baya an yi shi ne a Masallacin Darul Hadith da ke unguwar Tudun Yola a Kano.

A cewar wata majiya, an daura auren ne ba tare da sanin mutane da yawa ba don guje maganganu.

Babu wani cikakken bayani game da auren zuwa lokacin hada wannan rahoto, sai dai majiyarmu ta tabbatar da cewa sarkin ba ya nan lokacin da aka daura auren a safiyar yau.

Sarkin mai shekaru 60 yana zaune da mace daya fiye da shekaru talatin, kuma suna da yara hudu a tsakaninsu.