‘Yansanda sun kwato makamai tare da Dala 255,000 a Kwara

0
112

Rundunar ‘yansandan jihar Kwara, ta samu nasarar kwato, makamai da harsasai da kuma zunzurutun kudi dala 255,000 daga wani da ake zargi a inda ‘yansandan ke binciken ababen hawa kan hanyar Bode zuwa Saadu a karamar hukumar Moro da ke jihar.

An kama bindiga AK-47 guda biyu da harsasai guda 70 da kuma kwanson harsashi guda 50 na AK-47 da kuma waya guda 11 da wasu guraye da layu.

Kamar yadda mai Magana da yawun rundunar ‘yansandan, SP Okasanmi Ajayi,ya bayyana a Ilorin, wanda ya ce, wannan abin ya faru ne a wurin da ‘yansanda ke duba a baben hawa a kan hanyar Bode zuwa Saadu.
Okasanmi ya ce, “Daga cikin babbar nasarar da suaka samu ta yin amfani da wannan dabara ita ce wadda suka samu ranar 31, Disamba 2022, a yankin Bode Sadu da ke karamar hukumar Moro, yayi ‘yansansa suka shiga yankin suka kama wani a kan babur kirar Bajaj.”

Mai magana da yawun ‘yansandan ya ce, ‘yansandan na ci gaba da kokarin ganin sun kama wanda ake zargin wanda kuma ke daya daga cikin masu garkuwa a wannan a garin Ekiti da Kogi da kuma wasu sassa na jihar Kwara.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar Kwara, ya yi alkawarin kakkabe dukkan wasu bata-garin da suka hana al’umma zama lafiya a dukkan fadin jihar. Sanna kuma ya yi wa al’ummar jihar Kwara fatan alheri, musamman a wannan sabuwar shekara da aka shiga, kamar yadda ya ce.