Hukumar hana sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA) ta ce ta kama wasu ƙwayoyi masu yawan gaske a jihohi 4 da ke ƙasar.
BBC ta ce, wata sanarwa da Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya sanya wa hannu wadda aka wallafa a shafin hukumar na yanar gizo, hukumar ta ce ta kama tabar wiwi da nauyinta ya kai kilo 3,975kgs da ƙwayar tramadol 58,200.
A samamen da jami’an hukumar suka kai jihohin Kaduna da Kano da Imo da kuma jihar Legas, ta ce ta kama mutum 11 da take zargi da hannu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hukumar ta ce mutanen na amfani da dabaru da dama wajen shigar da ƙwaya Nijeriya tare da fitar da ita zuwa ƙasashen waje irin su Birtaniya da dubai.
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yaba wa jami’an hukumar a waɗannan jihohi bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen wannan kame.