Boko Haram sun kashe mayakan ISWAP 35 a tafkin Chadi

0
114

Rahotanni sun bayyana cewa, mayakan Boko Haram sun kashe mayakan ISWAP 35 bayan wani kazamin fada da ya barke tsakanin su a yankin tafkin Chadi.

Wata majiya ta shaida cewa rikicin ya biyo bayan wasu munanan hare-hare da mayakan Boko Haram suka kai a karkashin wasu fitattun kwamandojin kungiyar biyar, musamman Abu Umaimah, a maboyar ISWAP.

A yayin gwabzawar da aka yi a tsibirin Toumbun Gini na tafkin Chadi, kungiyar Boko Haram ta kwace makamai masu yawa daga hannun mayakan na ISWAP tare da fatattakarsu daga maboyarsu.

Wata majiyar kuma ta shaida cewa, ci gaba da hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa ne ya sanya manyan shugabannin ISWAP suka gudanar da taro a Tumbun Murhu domin tattauna gazawar kungiyar wajen kai manyan hare-hare a lokacin bukukuwan Kirisimati da sabuwar shekara kamar yadda suka tsara tun farko.

An tattaro cewa kungiyar ta ISWAP ta gaza kai hare-haren ne sabida munanan arangama da suke yi da takwararta, kungiyar Boko Haram.