Gwamnatin tarayya za ta fara mayar da kashin dabbobi zuwa takin zamani

0
91

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta shirya tsaf, domin mayar da wasu ababen da aka fitar daga jikin dabbobin da aka yanka a mayankar kamar su kashinsu da saurasu zuwa takin zamani.

Rajistaran cibiyar kula da muhallin kiwon lafiya ta kasa (EHCN) Dakta Yakubu Baba ne ya bayyana hakan a wata hirasa da Kamfanin dillancin labarai da ke babban birnin tarayya Abuja.

Dakta Yakubu ya ci gaba da cewa, cibiyar za ta fito da mafita inda za a rinka yin amfani da wasu ababen da aka fitar daga jikin dabbobin da aka yanka a mayankar domin sarrafa su zuwa takin zamani, inda ya kara da cewa, ana shirin yin hakan ne domin a kara samar wa da manoman kasar nan takin zamani.

“Cibiyar za ta fito da mafita inda za a rinka yin amfani da wasu ababen da aka fitar daga jikin dabbobin da aka yanka a mayankar domin sarrafa su zuwa takin zamani, inda ya kara da cewa, ana shirin yin hakan ne domin a kara samar wa da manoman kasar da takin zamani”.

A cewar Dakta Yakubu, cibiyar za ta tabbatar da an yi amfani da abababen da ake fitar wa daga jikin dabbobin da aka yanka domin ganin ba a zubar da su, inda za a mayar da su zuwa takin zamani domin amfanin manoman da ke a kasar nan.

Dakta Yakubu ya kara da cewa, idan an sarrafa ababen da aka fitar da su daga jikin dabbobin da aka yanka aka kuma sarrafa zuwa takin na zamani, za a rinka sayar wa da manoman ne.

“Idan an sarrafa abubuwan da aka fitar da su daga jikin dabbobin da aka yanka aka kuma sarrafa zuwa takin na zamani, za a rinka sayar wa da manoman ne cikin sauki, saboda haka manoman za su samu damar mallakar takin da za su yi amfani da shi, cikin sauki da kuma araha wamda kuma hakan zai taimaka wajem kara fadada noman da wadata kasa da abinci”.