Kocin Manchester United Erik Ten Hag, ya gargadi ‘yan wasan sa

0
121

Kocin Manchester United Erik ten Hag, ya gargadi ‘yan wasansa cewa zai ci gaba da hukunta duk wanda ya saba masa.

A kwanaki, Ten Hag ya kori Cristiano Ronaldo daga tawagarsa kuma daga karshe ya amince da soke kwantiragin dan wasan mai shekaru 37.

Kwanan nan, tsohon kocin Ajax din ya hukunta Marcus Rashford saboda ya makara a taron kungiyar.

Ya kuma hukunta dan wasa Alejandro Garnacho a lokacin wasannin kawance na kafin a fara wasannin Firimiya.

“Idan ana son a samu nasarar hadin da kirkirar halaye da al’adu masu nasara, to dole a bi ta wannan hanya a ra’ayina.

“Kowa zai ce zai bi irin hanyarsa idan ba a koya musu bin dokar kungiya ba, idan ba mu kafa ka’idoji da dabi’u masu kyau ba wajen kafa kungiya mai inganci da hadin kai ba, kuskuren kin yin hakan, zai dawo ne kan kungiyar ta hanyar samun rashin nasarori a wasanninmu,”in ji Ten Hag.