Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da yar ta a Kano

0
119

Wani matashi ɗan shekara 20, mai suna Gaddafi Sagir, ya kashe kishiyar mahaifiyarsa mai suna Rabi da kuma yar ta, Munawwara a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da misalin ƙarfe 10 ma dare a unguwar Fadama da ke Rijiyar Zaki a jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matashin na zargin marigayiya Rabi da yin sanadiyyar rabuwa da mahaifinsa, shi ne ya buga mata ƙarfe a wuya da goshi, nan take ta faɗi ta rasu da tsohon ciki a jikin ta.

Rundunar ƴan sanda a Kano, ta bakin kakakin ta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kiyawa ya ƙara da cewa yanzu haka rundunar ta kama wanda ake zargin, inda ya ce a yayin binciken farko, ya amsa cewa shi ne ya kashe mamatan.