Yadda za a zamanantar da harkar ilimi a Najeriya

0
105

Shafin da ke bawa kowa damar tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya shige masa duhu na rayuwa. A yau shafin na dauke da bayanin Abba Abubakar Yakubu, inda ya fara da cewa.

Muhawara game da wanda ya fi muhimmanci tsakanin kwarewa kan wani fannin rayuwa ko fasaha, da ingancin shaidar kammala karatu, ba yau aka fara ba. An dade tsakanin manazarta, masana harkokin koyarwa, da masu nazarin ci gaban rayuwa suna bayyana ra’ayoyin su game da abin da ya fi dacewa ana bai wa fifiko, don ya dace da ci gaban rayuwa da ake samu.

Tambayar da akasari aka fi yi ita ce, wanne tsarin koyarwa ya fi dacewa da zamani? Wacce manufa ake da ita wajen koyar da ilimi? Wacce rayuwa ake so daliban da ke karatu a manyan makarantun ilimi za su yi bayan sun kammala karatunsu na Jami’a ko Kwalejojin Kimiyya da Fasaha, da sauran cibiyoyin ilimi.

A yayin da wasu ke ganin mutum ya shiga makaranta, ya yi jarabawa, ya samu shaidar kammala karatu, shi ne ginshikin samun kowanne ilimi, wasu na ganin samun shaidar karatu don kawai dalibi ya cika wasu sharudda na makaranta ko ya shafe tsawon wasu shekaru yana koyon wani fanni na ilimi, bai wadatar ya zama mai ilimi ba, matukar abin da ya koya ba ya iya aiki da shi don inganta rayuwar sa ko ta wasu.

A Nijeriya ba sabon abu ba ne ka ga wanda ya karanta ilimin harkokin gona ko zana taswirar kasa da gine gine, yana aiki a banki, aikin jarida ko dai wani aikin ofis na wata ma’aikata, inda sam aikinsa bai shafi karatun da ya yi ba.

Abin da aka fi mayar da hankali kawai shi ne an kammala makaranta an samu shaidar kammala Digiri ko makamancinsa, za a je a nemi aiki da kwalin karatu, ko ma wanne iri ne. Abin da wasu ke korafi a kai shi ne wasu darussa ko kwasa kwasan da ake koyar da su a makarantu suna bukatar kwaskwarima, ko sabunta fasalinsu, don su dace da ci gaban rayuwa da canjin zamani.

Wasu kwasa kwasan da ake koyarwa a manyan makarantun kasar nan, ba su da wadatattun takardun karatu ko kayan gwaji, sai dai dogon turancin kawai ake koya musu daga tsofaffin takardun koyarwa, ko kuma su daliban su hada kudi su nemi kayan gwaji su koyawa kansu, don samun shaidar kammala karatu, ba tare da sun samu gogewar da ta kamata ba. Ga shi kuma an haifar da wata gasa ko kishi tsakanin daliban jami’o’i da na kwalejojin kimiyya da fasaha, inda ake ganin martabar digiri fiye da ta Babbar Diploma ta kasa (HND). Alhalin makarantun koyar da sana’o’i da kerekere su ne suka fi mayar da hankali wajen koyar da ilimin da dalibai za su iya rike kansu har bayan makaranta.

A shekarar da ta gabata wasu dalibai da ke shekarar karshe ta karatunsu na digirin farko a sashin nazarin koyar da ilimin injiniyancin kerekere a Jami’ar Jos, sun kera wata karamar mota samfurin motocin tsere da suka sanyawa suna Espera, domin samun shaidar kammala karatunsu na sashin Injiniyanci.

Amma abin takaicin shi ne; Daliban ba su iya hada komai a dakin su na gwaje-gwaje da ke Jami’ar ba, sai da suka je kamfanin wani mai kere-kere kafin suka iya kera motar da suka gabatar da samfurinta. Wadannan dalibai misali ne na irin halin da daliban ke fuskanta a kasar nan, saboda akasari karatun da suke yi na karatu ne kawai ake koya musu a aji ba a hadawa da gwaje-gwajen da za su tabbatar da ingancin karatun da suka yi.

Abin da ya sa wasu ke tunanin ba sa bukatar sai sun yi karatu mai zurfi ko digiri, matukar suna ganin suna da basirar kirkirar wasu abubuwa da kwarewar da suke da ita. Sai dai a kasa kamar a Nijeriya inda ake fifita shaidar kammala karatu abu ne mai wuya, mutum ya samu aiki ko wani tallafi ba tare da shaida ba. Abin da masana ke faɗa shi ne, koyar da ilimin da zai bai wa dalibi damar yin tunanin sarrafa wani abu ko kirkira da za ta kawo canji ko ci gaba a rayuwar jama’a, ta hanyar aiki da ilimin da ya koya da taimakon malaminsa. Ilimin da zai mayar da dalibi ya zama kadara da al’umma za ta amfana da iliminsa shi ne muhimmin abin da yanzu zamani ke nema, shi ne kuma sabon tsarin koyarwar da wasu kasashe suke runguma, don koyar da ‘yan kasashensu da ma ‘yan wasu kasashen kamar Nijeriya, inda sai ‘ya’yan masu hali ne kawai suke samun wannan damar.

Ko da yake mu a nan Nijeriya ba mu ba da muhimmanci ga wannan tsarin ba, amma mahukunta a Ma’aikatar Ilimi ta kasa ta fitar da wani tsari da zai inganta yadda ake koyar da ilimin kimiyya da fasaha da kuma kirkira a makarantu, tun daga matakin firamare zuwa jami’a, da kuma darasin koyar fara sana’a da bude kasuwanci, tsarin da a gajarce ake cewa, ‘STEAM’. Domin Gwamnatin Tarayya ta lura cewa, bayan ba za ta iya samar wa dukkan ‘yan kasa ayyukan yi ba, haka kuma ta lura da yadda talauci da rashin ayyukan yi ke barazana ga ci gaban kasar nan.

A saboda haka gwamnati ke kokarin ganin an samar da horo da kayan aiki ba kawai don koyar da dalibai ba, har ma da horar da malaman da suke koyar da daliban ta yadda za su samu saukin koyarwa cikin wannan sabon tsarin.

A sakamakon wannan sabon sauyi, masana harkokin ilimi na ganin hatta tsohon tsarin yadda ake koyarwa, malami a gaban aji shi ma ya kamata a sauya shi. Abin da ake so shi ne a samar da tsarin yadda dalibi da malami za su yi aiki tare wajen kirkiro wani abu, da sarrafa shi a aikace, ba tare da dogon turanci ba.

Wannan na nuni da cewa, idan har gwamnati za ta mayar da tsarin makarantun kasar nan bisa irin wannan salon koyarwar, tare da inganta yanayin muhallin koyarwa za a samu canji a yanayin ingancin ilimin da ake koyarwa, da kuma irin matasan da suke kammala karatu, ta yadda ba za su gama karatu su zama nauyi a wuyan gwamnati ba. Ilimin sana’o’in ko kasuwanci, da suka shafi sarrafa kwamfiyuta, noman zamani, kafinta, gyaran waya da gine-gine, ajin kwalliyar mata da girke-girke, duk za su samar da matasa masu dogaro da kai da ilimi mai gina al’umma.

Har wa yau kalubale ne kan gwamnati ta farfado da makarantunta na koyar sana’o’i da kere-kere, don cimma manufar gwamnati na sauya akalar koyarwa da yaki da rashin ayyukan yi. Ko da yake babban kalubalen da ake fuskanta a kasar nan, ba rashin sanin dabarun aiki ko mai ya kamata a yi ba ne.

A’a, rashin mayar da hankalin ‘yan siyasa da masu mulki n, kan abubuwan da suka shafi raya kasa da ci gaban jama’a.

Don haka yanzu da gwamnati ta waiwayo wannan bangaren ya kamata a yi da gaske, don ganin an dauki matakan da suka dace na kawo bunkasar ilimi da amfani da bai wa yawan matasa masu kwazo da muke da su, don kawo ci gaban masana’antu da kere-kere.