Wasu ‘yan bindiga sun bude wa jami’an NDLEA wuta a Legas

0
97

Wasu mutane dauke da makamai, a daren Litinin, sun bude wuta kan jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, a kan hanyar Awolowo, a yunkurinsu na hana su cafke direban babbar mota da ke dauke da buhunan tabar wiwi.

Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa, ‘yan bindigar da ake kyautata zaton na wata hukumar tsaro ne da ba a tantance ba, sun kuma fasa daya daga cikin motocin da hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ke aiki da su.

Sai dai kuma shiga tsakani da wasu sojoji suka yi, ya hana abin da zai haifar da wankan jini, yayin da ‘yan bindigar suka gudu tare da direban motar, inda suka yi watsi da motar.