‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro da dama a Kaduna

0
86

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, inda suka kashe jami’an tsaro da dama da suka hada da ‘yan sanda, sojoji da kuma ‘yan banga a wani shingen bincike a ranar Lahadi.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Kakangi, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa al’ummomin da abin ya shafa su ne kauyukan Kubau da Unguwan Zakara na karamar hukumar.

A cewar Kakangi, ‘yan bindigar sun kulla yarjejeniya da manoman yankin a matsayin riga-kafi don bai wa mazauna yankin damar zuwa gonakinsu.

Sai dai ‘yan bindigar su kan bi ta kauyuka suna sayar da shanun da suka yi karo da su, lamarin da ya sanya jami’an tsaro tada girar sama.

A cewarsa, “Mako uku da suka gabata jami’an tsaro sun kashe wani yaro da ke kula da shanunsu (’yan bindiga), ba su ji dadin kashe yaron ba.

“Sai a jiya (Lahadi) ‘yan ta’addan sun kai hari a shingen bincike na Aka da ke kan titin Birnin-Gwari zuwa Kakangi zuwa Randagi a yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari, inda suka farmaki duk wanda suka gani ciki har da jami’an tsaro.

“An kai harin ne da misalin karfe 2:00 na rana, ‘yan bindigar sun raba kawunansu gida biyu kuma sun kai harin a lokaci guda a kauyukan biyu, inda suka kashe jami’an tsaro da dama da suka hada da Civil Defence, ‘yansanda, ‘yan banga da sojoji.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar ‘yansanda ko wasu jami’an tsaro ko ma gwamnatin Jihar Kaduna kan lamarin.

A halin da ake ciki kuma, kiran da aka yi wa kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Muhammed Jalige, bai amsa ba.