An baiwa iyalan ‘yan sandan da suka rasa ransu a bakin aiki Naira miliyan 43 a Anambra

0
118

Iyalan ‘yansanda 20 da suka rasa rayukansu a Jihar Anambra sun karbi diyyar Naira miliyan 43.

Kwamishinan ‘yansandan Jihar Anambra, Mista Echeng Echeng ne, ya mika musu kudin a ranar Talata a hedikwatar rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra.

Leadership Hausa ta samu labarin cewa babban Sufeton-Janar din ‘yansandan ne ya umarci biyan tsarin inshorar iyalin don biyan kudin diyyar.

Yawan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan ofisoshin ‘yansanda da shingayen binciken ababen hawa ya janyo asarar rayukan ‘yan sandan da ba a taba ganin irinsa ba a jihar a ‘yan kwanakin nan.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga wanda ya bayyana cikakken bayani game da biyan diyyar, ya ce matakin wani shiri ne na Sufeto-Janar din ‘yan sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali, domin kara kwarin gwiwar jami’an yaki da masu aikata laifuka.