Mun biya Naira biliyan 173.2 kudin daidaita farashin man fetur cikin shekara 4 – Gwamnati

0
105

Wasu bayanai da suka fito daga Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, ta ce g5wamnatin Tarayya, ta bayar da kusan Naira biliyan 173.2 domin daidaita farashin sama da lita biliyan 11.6 na man fetur tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022.

Gwamnatin Tarayya na biyan kudin daidaita farashin man ne ta hanyar hukumar da ke kula da hada-hadar kasuwancin man fetur ta kasa.

Hukumar Kayyade Farashin Man Fetur (NMDPRA), ce ke tabbatar da daidata farashin man ta hanyar biyan kudin dakon man a manyan motoci zuwa gidajen mai.

Sai dai duk da wadannan maduden biliyoyin kudi da hukumar ke kashewa domin daidaita farashin, har yanzu ana sayar da man a mabambantan farashi a fadin kasar nan.

Wani abun takaici shi ne wasu gidajen man na boye man don samun damar sayar da shi sama da yadda gwamnati ta bayar da farashi.