‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 a Anambra

0
104

Wasu ‘yan bindiga dadi sun kashe mutum hudu a Nzomiwu da ke yankin Eziani a karamar hukumar Ihiala a Jihar Anambra.

An tattaro cewa ‘yan bindigan sun mamaye yankin ne a ranar Talata kuma suka fara harbin sama, inda a hakan suka kashe maza uku da mace daya wacce ma take dauke da juna biyu.

Ba a iya gano dalilin kisan ba zuwa yanzu, amma wata majiya daga yankin na cewa ‘yan bindigan cikin gaggawa suka arce bayan da suka yi kisan.

Majiyar na cewa, harbin da ‘yan bindigan suka yi shi ne ya janyo kisan mutum hudu.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce, gawarwakin mamata an kaisu zuwa dakin adana gawarwaki.