Jam’iyyun APC da NNPP na mayar wa da juna martani kan sabbin masarautun Kano

0
123

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa dawowa da tsohon tsarin masarautar Kano da dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudurin yi idan ya lashe zabe, hakan na nufin zai yi yaki da dokar da ta kafa sabbin masarautun da kuma shawarwarin al’umma.

Gwamnatin APC mai mulki a Kano karkashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta kirkiro sabbin masarautu guda biyar daga tsohuwar Masarautar Kano tare da cire wani da nada wani sabon sarki a 2019. Sabbin masarautun sun hada da Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Sai dai rahotannin da ke yawo cikin mutanen jihar na cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa zai soke sabbin Masarautun ya mayar da tsohon tsarin masarautar ta Kano.

Da yake mayar da martani kan hakan, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na kwamitin yakin neman zaben Gawuna/Garo, Malam Muhammad Garba, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, an bi tsarin da ya dace kafin majalisar dokokin jihar ta tabbatar da sabon tsarin masarautun.