Masarautar Zazzau ta kori wani dogari bisa aikata badala

0
255

Majalisan Masarautan Zazzau karkashin Jagoranci Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ta bayar da umurnin Koran Malam Sama’ila Abubakar Rimin Tsiwa daya daga cikin dogaran fadar Zazzau daga aiki a Masarautan Zazzau.

Wata matashiya wanda take shirin Aure tazo Fadan Zazzau domin a sadata da Mai Martaba Sarkin Zazzau bisa neman taimako kan batun auren ta sai ta gabatar da bayanan ta ga Malam Sama’ila wanda maimakon gabatar da ita zuwa inda ya kamata, sai ya yaudareta zuwa wani wuri dabam inda shi da Abokansa suka yi lalata da ita.

Majalisan Masarautan Zazzau, ta umurci Rundunan ‘Yan Sanda da ta gaggauta kamalla bincike, kuma su gabatar da masu laifi cikin gaggawa a gaban Kotu domin yanke masu hukuncin dai-dai da laifinsu.