Ka da a mika ragamar mulkin Najeriya a hannun mara lafiya – Peter Obi

0
95

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bukaci ‘yan Nijeriya ka da su zabi dan takarar da bai da cikakkiyar lafiya a zaben 2023.

Obi wanda ya yi wannan kiran a yau Alhamis a taron tsofaffin dalibai na Jami’ar Nsukka da ke a Enugu, inda ya yi nuni da cewa, ganin Nijeriya a yanzu ba ta cikin kwanciyar hankali bai kamata ‘yan Nijeriya su zabi wanda bai da lafiya ba.

Obi ya kara da cewa, bai kamata ‘yan Nijeriya su kada wa wanda ba zai iya shafe mintuna 30 a tsaye ba.

Ya ci gaba da cewa, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi duba ga wanda aka fi aminta da shi a zaben na shugaban kasa, mussaman don a kaucewa sake jefa kasar nan cikin wata sabuwar matsala.

A cewarsa, “Ba wai na ce wani bai da lafiya bane, mun kuma shafe sama da awa biyu a nan, amma ba ma son mutanen da ba za sa iya shafe mintuna 30 a tsaye ba.”

Ya ce, a lokacin zabuka a Kasar Amurka suna gudanar da yin gasa a tsakanin ‘yan takararsu, inda har wani ya yi wa tsohon shugaban kasar tambaya ta daban wacce kuma ya amsa ta.

Obi, ya yi nuni da cewa, amma a nan Nijeriya, wani yana son tsayawa takara, amma bamu san adadin shekarunsa na haihuwa ba, cikakken sunansa da kuma makarantun da ya yi ba, inda ya kara da cewa, babu wanda ya san asalinsa amma ya dage sai ya shugabanci kasar nan.