Tufka da warwarar INEC kan yiwuwar zaben 2023

0
143

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi wa ‘Yan Nijeriya ba-zata a farkon wannan makon yayin da ta bayyana shakku kan yiwuwar zaben 2023, lamarin da ya zama tufka da warwara dangane da alwashi da kuma tabbacin da ta yi ta bai wa ‘Yan Nijeriyar har ma da ‘yan kasashen waje masu muradin sa ido a zaben dangane da gudanar da shi kamar yadda aka tsara.

Ga dukkan alamu, wannan tufka da warwara na iya mayar da hannun agogo baya game da zaben na 2023, sakamakon yadda barazanar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa.

A wannan shekarar, babu wani abu mai muhimmanci musamman a sulusin shekarar na farko a Nijeriya da hankula suka karkata a kai kamar zaben 2023. Inda kowa ya zuba ido ya ga yadda Hukumar Zaben Mai Kanta ta Kasa (INEC) za ta gudanar da sahihin zabe domin tabbatar da an bai wa ‘Yan Nijeriya shugabannin da suka zaba da hannunsu.

Sai dai kuma, galibin ‘Yan Nijeriya da ke tsumayar zaben domin samun sauyin gwamnati musamman saboda halin da kasar ke ciki, sun shiga dimuwa da suka ji bayanin INEC a farkon wannan makon cewa, da yiwuwar a soke zaben na 2023 matukar ba a shawo kan matsar tsaron da ke addabar yankuna daban-daban na kasar nan ba.
Idan za a iya tunawa, a watan Nuwambar 2022, LEADERSHIP Hausa ta ruwaito masana na ankararwa game da yadda rashin tsaro ke baranaza ga yiwuwar gudanar da zaben 2023 wanda ita kuma INEC ta sha fitowa fili tana bayanin cewa babu wata barazanar tsaro da za ta hana gudanar da zaben.

An ruwaito shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yana cewa duk da wadannan fafafen hare-hare hukumar za ta gudanar da sahihin zabe a 2023. Ya bayar da tabbacin ne a lokacin da yake jawabi a Jihar Ogun.
Haka kuma INEC ta bayyana cewa babu gudu babu ja da baya wajen gudanar da zabe a dukkan kananan hukumomi 774 da ke fadin Nijeriya.

Mai Magana da yawan hukumar INEC, Mista Rotimi ya yi karin hasken cewa, “Mun samu tabbaci daga wurin hukumomin tsaro wadanda suka hada da sojoji da masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin an gudanar da zabe.

“Wannanin zabe shi ne zai tabbatar da dorewar kasarmu kuma kowa ya san haka. Bukatuwa ta karu, sannan wannan shi ne karo na farko da yawan mutane za su yi zabe.”

Sai dai kuma, bayan da INEC ta ba da wannan tabbaci, shugabanni addinai da suka fahimci girman matsalar rashin tsaron da Nijeriya ke ka-ka-ni-ka-yi a ciki, ba su gamsu da wannan ikirrari na INEC ba, inda suka fito fili suka sake jaddada cewa, kar fa a kuskura a bari baranazanar ta tsaro ta hana gudanar da zaben 2023.
A ranar 9 ga watan Disambar 2022, LEADERSHIP Hausa ta ruwaito mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, yana bayanin cewa, “Komin runtsi dole a yi zaben 2023, duk da tsananin farkaki da ake kai wa ofisoshin INEC.”

Ya bayyana hakan ne a Abuja lokacin taron majalisar hadaka ta addinan Nijeriya (NIREC).
A nashi bangaren, Shugaban Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), Arhbishop Daniel C. Okoh ya bayyana cewa a daidai lokacin da kasar nan ke fuskantar zaben 2023, an samu tambayoyi masu yawa da kuma shakku kan yadda Nijeriya za ta iya gudanar da sahihin zabe.

Wannan barazanar tsaron dai ta dade tana jefa mutane cikin rudani game da zaben na 2023, domin kamar yadda LEADERSHIP Hausa ta ruwaito a watan Nuwamba, an kai wa ofisoshin INEC guda uku hari a jihohin Ogun, Osun da kuma Ebonyi. Haka kuma a cikin wata hudu, an banka wuta a wasu ofisoshin INEC guda bakwai a Jihar Imo.
Yayin da farmakin jihohin Ogun da Osun suka fara a ranar 10 ga watan Nuwambar 2022, sannan an kai farmaki a jihohin Ebonyi da Imo a ranar 26 ga watan Nuwamba zuwa ranar 1 ga watan Disamba. Wadannan alkaluman farmakin da aka lissafo sun yi sanadiyyar rasa muhimman kayayyaki da za a yi amfani da su a babban zaben 2023.
A ofishin INEC na Jihar Ogun, an kone akwatunan zabe guda 904 da katukan jefa kuri’a wadanda ba a amsa ba guda 65,699 da rumfunan zabe 29 da jakunkunan zabe 57 da kuma janareta guda uku.

A farmakin da aka kai wa ofishin INEC a karamar hukumar Izzi da ke Jihar Ebonyi, kamar yadda kakakin INEC, Festus Okoye ya fada, an babbake akwatunan zabe guda 340, da rumfunan zabe 130, da janareta 14 da mayan tankokin ruwa da kujeru da katunan jefa kuri’a wanda har yanzu ba a san adadinsu ba.
LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa an fi samun hare-hare a ofisoshin INEC da ke yankin kudu maso gabashin Nijeriya.
To sai dai kuma, da alama, INEC ta saduda, inda ta yi tufka da warwara a kan jaruntar da ta so nunawa ta zama ki-fadi a kan barazanar da rashin tsaron ke yi ga zaben 2023, inda ta fito baro-baro a fili a wannan makon ta ayyana cewa idan har ba a dakile yawaitar rashin tsaro ba, akwai yuwuwar soke zaben 2023 ko kuma a dage shi.
INEC ta yi wannan gargadi ne a daidai lokacin da ya rage kasa da wata biyu a gudanar da zabe, inda ake kara samun barazanar tsaro mai zafi a wasu sassan kasar nan.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya samu wakilcin shugaban cibiyan nazarin zabe (BEI), Farfesa Abdullahi Abdu Zuru, ya bayyana hakan Abuja wurin taron horar da jami’an zabe.
Shugaban hukumar ya jadda cewa dole ne jami’an tsaro su dauki matakin kare dukkan jami’an zabe da kayayyakin aiki kasancewarsu masu lura da harkokin tsaro a kasa, sannan su kasance da cikakken kayayyakin aiki domin tunkarar duk wani kalubale.
“Dukkanmu mun amincewa cewa tsaro lokacin zabe yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dimokuradyya ta hanyar samar da sahihin zabe da kuma karfafa tsarin shi kan shi zaben.
“Saboda haka, a shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2023, hukumar tana kira da a sauya salo wajen tabbatar da kare jami’an zabe da kayayyaki da kuma tsare-tsare.
“Wannan yana da matukar muhimmanci ga hukumar idan aka yi la’akari da kalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan daban-daban na kasar nan, kuma masu yi wa kasa hidima su suka kasance jigon jami’an zabe a dukkan rumfanan zabe.
“Bugu da kari, idan ba a dauki kwararan matakai kan rashin tsaro ba, to za a iya kai wa ga sokewa ko dage zabe a mazabun da za su kawo cikas wajen bayyana sakamaon zabe da kuma haddasa rikicin shugabanci. Doke a dauki matakin hana afkuwan hakan, sannan kar a sake a bar hakan ya faru.”
Yanzu haka dai, ‘Yan Nijeriya sun kara shiga dimuwa, domin a yayin da suka kasa suka tsare suna fatan ganin sabbin shugabannin da za su karbi ragamar mulki da nufin magance tarin matsalolin da ke addabar kasar yanzu haka, da alama murnarsu na shirin komawa ciki, saboda wannan gargadi da INEC ta yi, duk kuwa da cewa mai bai wa shugaban kasa shawara a kan tsaron kasa (NSA), Janar Mohammed Babagana Monguno (mai ritaya) tare da Sufeto Janar na ‘Yansanda sun ba da tabbacin babu abin da zai faru, za a yi zaben na 2023 lami lafiya.
Monguno ya kara da cewa akwai sabon tsarin dokar zabe da zai jagoranci zaben 2023, sakamakon gyaran dokar zaben a 2022 wanda ya sa aka kara yin nazari kan dokokin INEC da ka’idojin gudanar da zabukan.
Ya ce, “Musamman sashi na 47 (2), 60 (1, 2 & 5), 62 (1), 64(4a & 4b) da 64 (5) na dokar zabe ta 2022, sun ya bai wa INEC ikon amfani da duk wata na’urar ta fasaha domin bayyana sakamakon zabe da tattance masu zabe.”

•Watakila Tarihi Ya Maimaita Kansa A Zaben
A wani bangaren kuma, ana ganin zaben na 2023, watakila tarihi ya maimaita kansa dangane da zaben 1979 wanda Alhaji Shehu Shagari ya lashe a karkashin jam’iyyar NPN. Galibin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben na 2023 ana ganin tamkar suna wakiltar kabilu ne da yankunansu. Daga yankin Yarabawa, akwai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a yankin Ibo akwai Peter Obi, yayin da a yankin arewa aka samu ‘yan takara guda biyu, Atiku Abubakar da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
A zaben 1979, an kafa jam’iyyun siyasa da yawa bisa la’akari da bambancin yankuna da yadda ya kamata masu jefa kuri’a su karkata ga ‘yan takara masu wakiltar yankunansu da kuma kabilunsu.
A wancen zabe, Shagari ya yi takara da Obafemi Awolowo na jam’iyyar UPN, da Nnamdi Azikiwe na jam’iyyar NPP da kuma Waziri Ibrahim na jam’iyyar GNPP.
Wasu masana harkokin siyasa da suka bayyana ra’ayoyinsu, suna kallon zaben zai kasance bisa bangaranci wanda zai bai wa kowani dan takara daga cikin manyan ‘yan takara damar lashe zabe.
Wani jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato, Kabiru Aliyu Gobirawa, ya yi hasashen yadda ‘yan Nijeriya za su kada kuri’a a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Da yake yin Allah wadai da dabi’u marasa kyau a cikin tsarin dimokuradiyya, ya dora laifin kan ‘yan siyasa da kuma yanke kauna kan iya kwace mulki daga hannnun manyan ‘yan siyasa.
Gobirawa ya kwatanta yanayin siyasar da ake ciki a halin yanzu da abin da ya faru a zaben shugaban kasa na 1979.
A cewarsa, “Kamar abin da ya faru a shekarar 1979, manyan ‘yan takarar shugaban kasa uku da suka hada da Alhaji Shehu Shagari, Cif Obafemi Awolowo da kuma Nnamdi Azikiwe dukkan su abun tunawa ne.
“Yan takarar guda ukun sun fito ne daga yankuna daban-daban, kuma akwai tsarin kada kuri’a a lokacin. Ina jin tsoro irin wannan lamari na iya kara faruwa, yayin da muke gudanar da zabe a wata mai zuwa bisa la’akari da cewa jiga-jigan ‘yan takarar shugaban kasa guda uku wato Abubakar Atiku, Bola Ahmed Tinubu da Peter Obi, suna ba da dimbin mabiya a yankunansu.
“Wannan abin la’akari ne a Nijeriya duba da yadda kasar ke da yankuna da kabilu masu yawa,” in ji Gobirawa.
Hasashe na nuna cewa Atiku da Kwankwaso na iya kacancana kuri’an junansu a yankin arewa wanda zai iya bai wa sauran ‘yan takarar damar cin karensu babu babbaka, musamman idan aka yi la’akari da Kano ce tafi yawan masu jefa kuri’a a yankin arewa wanda za ta iya yanke hukunci.
Wani mai sharhi kan harkokin siyasa na kungiyar matasa masu fafutukar tabbatar da shugabanci nagari, Aminu Haruna Maipompo ya tantance wanda zai iya samun nasara a tsakanin manyan ‘yan takara guda biyu a arewa, Atiku na jam’iyyar PDP da Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.
Ya ce, “A bayyana yake cewa Atiku na iya samun nasara kan Kwankwaso, saboda akwai yuwuwar Atiku zai iya samun kashi 25 a dukkan jihohin arewa guda 19, yayin da watakila Kwankwaso na iya samun kashi 25 a jihohi bakwai na arewa. Domin kuwa Kwankwaso ba zai iya samun kashi 25 da ake bukata ba a dukkan jihohin arewa ta tsakiya ba.
“A karshe, Atiku zai doke Kwankwaso da tazara mai yawa a yankin arewacin Nijeriya.”
A cewar manazarcin al’amurar siyasa daga Jihar Kaduna, Yerima Shettima, idan har aka gudanar da zaben bisa la’akari da yankuna, za a samu wanda ya lashe zaben amma kuma ba da wasu kuri’u masu yawa ba. Ya ce haka zai iya haddasa muhawara a kasa, saboda idan har Yarbawa suka yanke shawarar zaben Tinubu na jam’iyyar APC, su ma Ibo za su zabi Peter Obi na jam’iyyar LP, sannan kuma Hausawa za su zabi ko dai Atiku na jam’iyyar PDP ko kuma Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, yayin da yankin arewa ta tsakiya ne zai yanke hukuncin wanda zai lashe zaben.
Alhaji Shettima wanda ya kasance shugaban kungiyar matasan arewa (AYCF), ya yi kira ga ‘yan Nijeriya kar su yi zabe bisa la’akari da yanki ko kabila ko addini, su yi kokarin zaban nagartaccen shugaban kasa.
Wani babban dan siyasa a Jihar Ribas, Hon. Innocent Ajaelu ya bayyana cewa idan har aka yi zaben 2023 bisa la’akari da yanki zai haddasa samun gurbatattun shugabanni.
Da yake yi wa LEADERSHIP karin bayani a Fatakwal, Ajaelu wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Oyigbo, ya siffanta zabe bisa la’akari da yankin ba tsarin dimokuradiyya ba ne.
Ajaelu ya ce a halin da ake ciki ‘Yan Nijeriya na bukatar samun nagartaccen shugaba da zai iya magance matsalolin kasar nan.