Sarkin Wusasa a masarautar Zazzau a Jihar Kaduna, Injiniya Isiyaku Dallami Yusufu, ya bayyana ci gaba da rungumar dokokin addini sau da kafa a tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista da cewar shi ne kawai zai kawo karshen matsalolin da suke addabar Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriya.
Sarkin Wusasa ya bayyana haka ne a tsakacin da ya yi na shigowar shekara ta 2023, ya ce ya kamar yadda da zarar watan yin kirisimeti ya tsaya, a nan ne za ka ga mabiya addinin kirista su na yin addini a kan lokaci, haka ma mabiya addinin musulunci lokacin watan Azumi, da zarar watannin da aka ambata sun wuce, sai a koma sharholiya da addinan biyun.
Ya kuma kara da cewa kamar yadda nabiya addinan biyu suke yin ibada da kuma addu’o’i a watanni biyun da aka ambata a baya, ya dace su ci gaba da yin Ibadan tare da yin addu’o’in da za su zama silar kawo karshen matsalolin rashin tsaro da suke addabar wasu jihohi arewacin Nijeriya.
Da kuma ya juya ga shugabannin addini da suke Nijeriya ba na arewacin Nijeriya kawai ba, a nan sai ya tunatar da su nauyin da ke kansu na bayyana wa shugabanni gaskiya a duk matsala da ta bayyana a gabansu.
Sarkin Wusasa ya yi kira ga ‘yan siyasa, musamman wadanda suka shiga takara a kowane matsayi da su amince Allah ke bayar da mulki a duk lokacin da ya so, ga kuma wanda ya so.