Makarantun Mali sun fara bai wa dalibai darasi na musamman kan kishin kasa

0
92

Sojin da ke mulki a Mali sun gabatar da wani sabon darasi a makarantun kasar wanda a cikinsa za a rika koyawa dalibai kishin kasa a wani yunkuri na sauya dabi’un al’umma da kuma kaucewa biyayya ga turawabn mulkin mallaka.

Wannan mataki na zuwa ne bayan kasar ta yammacin Afrika ta katse mu’amalar da ke tsakaninta da uwar goyonta Faransa sakamakon zarge-zargen cewa Paris na taimakawa wajen kaddamar da hare-haren ta’addanci a cikin kasar mai fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ruwaito cewa Firaminista Choguel Kokalla Maiga da kansa ya halarci zaman bayar da darasin na farko da ya gudana a dakin ‘yanci da ke cikin kwalejin kimiyya ta birnin Bamako wanda a nan ne kasar ta sanar da karbar ‘yancinta ranar 22 ga watan Satumban 1960.

Manufar bayar da darasin shi ne ankarar da jama’a game da muhimmancin kishin kasa musamman dai dai lokacin da ake amfani da ‘yan asalin kasar wajen wargaza ta.

An shirya fara bayar da darasin na kishin kasa a yau asabar ne don samar da wata rana ta musamman da za a rika tunawa da ita wato ‘‘Ranar kishin kasa da Sadaukarwa’’kamar yadda shugaban mulkin Soji Assimi Goita ya sanar.

A watan Agustan 2020 ne Goita ya karbe ragamar mulkin kasar da karfi ta hanyar juyin mulki lamarin da ya janyo kasar suka da kuma takunkumi daga manyan kasashen Duniya ciki har da kungiyar ECOWAS da AU musamman bayan sanarwar Sojin kan shirin ci gaba da jan ragamar kasar a shekaru 5 masu zuwa.

Sai dai bayan tsanantar takunkumi da kuma kullewa kasar iyakokinta da kasashen makwabta a ranar 14 ga watan Janairun 2022 al’ummar kasar sun gudanar da wata kakkarfar zanga-zangar kasa baki daya don goyon bayan ci gaba da kasancewar Sojojin akan madafun iko duk da matsin lambar.

Gwamnatin Sojin ta yi amannar cewa wannan zanga-zanga ta ranar 14 ga Janairun 2022 ta taimaka matuka wajen gamsar da jama’a muhimmancin kishin kasa dama baiwa Sojojin kwarin gwiwar ci gaba da jan ragamar Mali.

Wannan dalili a cewar gwamnatin ya sanya za a fara amfani da kowacce ranar 14 ga watan Janairu don zamowa ranar kishin kasa da sadaukarwa ga al’ummar ta Mali.