NNPC za ta fara aikin hakar man fetur a jihar Nasarawa cikin watan Maris

0
103

Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya sanar da shirin fara hakar man fetur a jihar Nassarawa da ke yankin arewacin kasar cikin watan Maris mai zuwa wanda ke matsayin karon farko da aka gano irin wannan albarkatu a jihar ta arewacin kasar.

Matakin gano rijiyar man a Nassarawa dai na zuwa ne a wani yunkuri da NNPC ke yi don lalubo sauran sassan kasar da ke da irin wannan albarkatun karkashin kasa a cikin Najeriyar.

Kamfanin na NNPC karkashin jagoranci Mele Kyari na ci gaba da baza koma don lalubo man fetur akan tsaudari sabanin cikin ruwa da abaya kasar ke lalube a yankin kudanci.

Lokacin da ya ke karbar bakoncin tawagar wakilcin al’ummar ta jihar Nassarawa karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule a shalkwatar kamfanin na NNPC da ke Abuja, Kyari ya bayar da tabbacin cewa kamfanin zai jagoranci aikin hakar man cikin watan Maris mai zuwa.

A watan Nuwamban bara ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar man fetur a jihohin Bauchi da Gombe shekaru 2 bayan sanar da gano albarkatun man a jihohin 2 na arewacin Najeriya irinsa na farko a tarihin kasar.