NSCDC ta yi bankwana da jami’anta 7 da ‘yan bindiga suka kashe a Kaduna

0
99

An yi Jana’izar Jami’an hukumar tsaro ta (NSCDC) guda bakwai da wasu ‘yan bindiga sun yi musu kwanton bauna suka kashe su a garin Birnin Gwari ranar Litinin, 9 ga watan Janairu, 2023 yayin da suke aiki a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

An mika gawarwakin nasu ga iyalai da ‘yan uwa a hukumar NSCDC da ke Kaduna bayan gabatar da faretin bankwana.

Babban Kwamandan Rundunar, Dakta Ahmed Abubakar Audi, ne ya yi bankwana da Jami’an yayin bankwana da su yayin taron ranar Asabar, 14 ga watan Janairu, a Ofishin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna.

Audi ya bayyana damuwarsa a yayin da yake jajantawa iyalai da abokan arziki da kuma ‘yan uwa kan wannan rashi da aka yi tare da yi musu addu’ar Allah ya jikansu.

Shugaban wanda ya samu wakilcin kwamandan rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Idris Yahaya Adah, ya yaba da kokarin jami’an da suka rasa rayukansu wajen kare kasar.