‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga 4 a Neja, tare da kwato makamai

0
104

‘Yansanda sun kashe ‘yan bindiga hudu, sun kama wasu mutane bakwai da ake zargi da satar mutane a Jihar Neja.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an kama wasu mutane bakwai bisa laifin fasa-kwauri da kuma ikirarin fashi da makami.

Abiodun ya bayyana cewa an samu kiran gaggawa ne a ranar 12 ga watan Janairu da misalin karfe 11:55 na safe daga kauyen Maje ta karamar hukumar Nasko Magama, inda wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne ke kokarin kutsawa wani gida a kauyen.

A yayin da jami’an ‘yansanda suka yi artabu da bindiga, wanda ya kai ga kashe wani dan bindiga guda daya, yayin da aka kwato bindigarsa kirar AK-49 daga wurin.

Wasu kuma sun tsere zuwa cikin dajin da raunukan harbin bindiga.

Har ila yau, a ranar 8 ga watan Janairu da misalin karfe 12:30 na rana, ‘yansanda sun kai daukin gaggawa yayin da wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne da suka yi garkuwa da wani direba kwanaki kadan a kan hanyar Kuka-Babanna, karamar hukumar New-Bussa Borgu, sun shirya karbar kudin fansa.

Rundunar hadin guiwa ta ‘yansanda da sojoji da ‘yan banga na yankin, an ce an kamo wadanda ake zargin zuwa wani dajin da ke kusa da inda ‘yan bindigar suka yi artabu da su, inda aka kashe ‘yan ta’adda uku, sannan wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.

An samu nasarar kwato bindiga guda daya dauke da harsashi hudu.