Shahararren dan wasan barkwanci Kamal Aboki ya rasu

0
451

Fittacen jarumin barkwanci wanda aka fi sani da Kamal Aboki ya rasu.

Sanadin mutuwar tashi ya faru ne ta wani mummunan hatsari da ya akfu a yammacin ranar litinin a garin Gaya dake jihar Kano, Yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga garin maiduguri.

Mummunan hatsarin ya ritsa da mutane 15 a cikin motar wanda dukansu Allah yayi musu rasuwa hardashi jarumi Kamal.

Jaridar Hausa24 ta tabbatar da rasuwar wannan jarumi ne bayan zantawa da tayi da dan uwansa me suna Usman ta wayar salula.

Haka zalika ya shaida mana cewa tabbas dan uwansa Kamal ya rasu a yammacin yau, kuma za’ayi janaizar sa gobe da safe a unguwar Kawo dake Hotoro a jihar Kano.