Ukraine zata samu karin makamai bayan mummunar harin Rasha – NATO

0
146

Kungiyar tsaro ta NATO ta bayyana cewa Ukraine na jiran tsammanin karin wasu manyan makamai daga kasashen yammacin duniya nan ba da dadewa ba, yayin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yabawa dakarunsa bayan da suka yi ikirarin kwace wani gari na Ukraine.

Sanarwar NATO ta ranar Lahadi na zuwa ne yayin da ake gudanar da wani gagarumin aikin ceto a wani hasumiya da ke gabashin birnin Dnipro, sakamakon harin makami mai linzami da Rasha ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30 tare da bacewar wasu 34.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi Allah wadai da yadda kasashen duniya suka yi gum kan harin, yana mai cewa Ukraine bata samu sakonnin juyayi daga sassan duniya kan wannan ta’addanci ba.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce Ukraine na iya sa ran karin manyan makamai biyo bayan bukatar da Kyiv ta yi wa kawayenta na motocin yaki, manyan bindigogi da makamai masu linzami da ta ce suna da muhimmanci wajen kare kanta.

Stoltenberg ya shaida wa jaridar Handelsblatt ta Jamus cewa, “alÆ™awuran baya-bayan nan na samar da manyan kayan yaÆ™i na da mahimmanci — kuma ina sa ran za a samu Æ™arin a nan ba da dadewa ba.