‘Yan bindiga sun kona wani limamin Katolika da ransa a Neja

0
146

‘Yan bindiga sun kona wani limamin cocin Katolica da ransa a karmar hukumar Paikoro ta jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

‘Yan bidigar sun isa gidan Rev. Fr Isaac Achi ne da misalin karfe 3 na asubahin Lahadi inda suka yi ta kokarin shiga gidan amma ba su samu nasara ba.

Ganin cewa sun gaza shiga gidan saboda manyan kofofi na tsaro masu karfe ya sa suka fusata har suka banka wa gidan wuta, kamar yadda rahotanni daga yankin suka bayyana.

Kafin mutuwar Reverend Father Achi yana aiki ne da  majami’ar Katolika ta  Saint Peters and Paul Catholic Church, Kafin-Koro,  a karamar hukumar Paikoro ta jihar Nejar.

Kakakin rundunar ‘yan sadan jihar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ‘yan bindigar sun raunata wani limamin Katolika a yayin harin.