‘Yan ta’addar da suka yi garkuwa da DPO a jihar Filato sun sake shi

0
116

Babban jami’in ‘yan sandan (DPO), SP Laree, wanda a kwanakin baya aka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Pankshin da ke jihar Filato ya samu ‘yancinsa kamar yadda iyalansa suka shaida.

An nakalto cewa SP Laree dai an yi garkuwa da shi ne a ranar Alhamis a wani otel da ke Pankshin ta tsakiya a jihar Filato.

An yi garkuwa da DPO kwanaki uku kacal da kama aiki a sabon wajen aikin da aka tura shi a matsayin DPO a Pankshin.

Sai dai babu cikakken bayanin kan nawa aka biya kudin fansa kuma nawa aka biya kafin sako DPO zuwa hada wannan rahoton.

Daya daga cikin ahlinsa da baya son sunansa ya bayyana a jarida ya shaida wa LEADERSHIP cewa tabbas jami’in ‘yansandan ya samu kubuta kuma har ya dawo cikin iyalansa.