Amurka ta cafke dan Najeriyar da ya damfari bankunanta

0
166

Wani dan Najeriya ya amsa laifin bude asusun ajiyar banki na bogi har guda 470 da ya yi amfani da su wajen damfarar bankunan Amurka da dama

Ahmed Ponle, dan Najeriyan mai shekaru 42, wanda kasurgumin dan damfara ne ya amsa tuhumar da ake masa ta damfarar bankuna a wata kotun lardi da ke New Jersey a watan Afrilun shekarar da ta gabata.

Yana fuskantar hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari sakamakon wannan laifi da ya shafi zambatar akalla bankunan Amurka 10 da  ke kunshe da kudi har dala  miliyan 6.

Yanzu alkalin kotun lardin, Noel Hillman ya sanya ranar 20 ga watan Janairu din nan a matsayin ranar da za a yanke wa Ponle hukunci, bayan jerin dage dage tun lokacin da ya amsa laifinsa a shekarar da ta gabata.

Masu bincike a Amurka sun bayyana ta wani kundi, yadda Ponle ya yi amfani da fasfunan bogi wajen bude akalla asusun ajiyar banki akalla 470 a rassan bankunan Amurka daban daban.

Ya yi amfani da fasfunan da ke dauke da hotonsa, amma kuma sunayen bogi ciki har da fasfunan Kenyan da Senegal.

Gwamnatin Amurka dai ta tabbatar da cewa, wannan dan taliki bai wahalal da hukuma ba, inda ya amsa laifinsa a ranar 7 ga watan Agustan shekarar 2022.