Sabuwar gwamnatin Najeriya za ta gaji bashin tiriliyan 77

0
141

Hukumar kula da Basussuka ta Najeriya ta bayyana cewar, sabuwar gwamnati mai zuwa a kasar za ta gaji bashin da ya kai Naira Tiriliyan 77.

Musamman ganin yadda gwamnatin a yanzu ke kokarin sake ciyo bashin da ya kai Naira tiriliyan 11 da biliyan 209 domin cike gibin da ake da shi a cikin kasafin kudi na wannan shekara.