An kama daya daga cikin ‘ya’yan shugabaan Equatorial Guinea kan zargin sa da sace tare da sayar da wani jirgin sama mallakin gwamnatin kasar.
An tsare Ruslan Obiang Nsue a ranar Litinin, sannan aka yi masa daurin talala kamar yadda kafar talabijin ta kasar ta bayyana.
Tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata, aka kaddamar da bincike bayan hukumomi sun gano cewa, daya daga cikin jiragen gwamnati mai lamba ATR 72-500 ya yi batan-dabo a filin jiragen sama na kasa da kasa.
A shekarar 2018 ne aka tura wannan jirgin zuwa kasar Spain domin kula da lafiyarsa, yayin da aka zargi Obiang da sayar da shi ga kamfanin Binter Technic, mai kula da lafiyar jirage a Las Palmas da ke tsibirin Grand Canary a Spain din.
Jirgin dai na daukar fasinjoji 74 kuma tun a tsakan-kanin shekara ta 1980, kamfanin ATR na hadin guiwa tsakanin Italiya da Faransa ya kera shi.
Da ma dai Equatorial Guine ta yi kaurin suna a fannin cin hanci da rashawa, inda kungiyar Transparency International ta ayyana ta a matsayin ta 172 daga cikin jerin kasashe 180 da suka fi kwarewa a rashawa a shekara ta 2021.
A bangare guda ana kallon mahaifinsa, shugaba Teodoro Obiang Nguema da yin mulkin kama-karya a kasar.