Ministan cikin gidan Ukraine ya mutu a wani hadarin jirgin sama

0
149

Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya fado da safiyar yau laraba a kusa da wata makaranta a yankin Kiev na kasar Ukraine,  hadarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 ciki har da ministan harkokin cikin gida da yara uku, wani sabon bala’i a Ukraine ‘yan kwanaki bayan wani kazamin harin da Rasha ta kai a Dnipro.

Da misalin karfe 10:30 na safiyar yau laraba, gwamnan yankin, Oleksiï Kouleba, ta hanyar Telegram ya bayyana mutuwar mutane 18  ciki har da yara 3.

Gwamnan yankin, Oleksiï Kouleba ya ce har ila yau akwai mutane 29 da suka jikkata, ciki har da yara 15, abin da ke kara fargabar za a iya samun asarar rayuka.

Ministan cikin gidan Ukraine da ya mutu a hadarin jirgin sama Denys Monastyrsky.Ministan cikin gidan Ukraine da ya mutu a hadarin jirgin sama Denys Monastyrsky.Ministan cikin gidan Ukraine da ya mutu a hadarin jirgin sama Denys Monastyrsky.Ministan cikin gidan Ukraine da ya mutu a hadarin jirgin sama Denys Monastyrsky.A kan hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta, ana ganin ragowar jirgin  gauraye da tarkace, kusa da wata mota da aka lalata karkashin nauyin karfe. Jami’an kashe gobara da ‘yan sanda suna wurin.

Daga cikin wadanda abin ya rutsa da su har da ministan harkokin cikin gida Denys Monastyrsky, dan shekaru 42, da mataimakinsa na farko Yevgeny Yenine, da kuma sakataren harkokin wajen ma’aikatar Yuriy Lubkovych, wadanda ke cikin jirgin tare da wasu mutane shida.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya bayyana alhininsa biyo ga al’ummar Ukraine bayan mutuwar ministan cikin gida, babban aminin kungiyar tarrayar Turai.