‘Yan bindiga sun kashe mutane 3 tare da raunata wasu a katsina

0
139

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Jajar Kanwa da ke karamar hukumar Jibia a Jihar Katsina, inda suka kashe mutane uku.

Wasu mazauna garin biyu ne ‘yan ta’addan suka jikkata, inda suka yi awon gaba da dabbobi tare da kwashe kudi, wayoyin hannu da abinci.

Wata majiya ta bayyana wa Leadership Hausa cewa, ‘yan ta’addan sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 2:00 na dare a kan babura, yayin da suke dauke da muggan makamai da suka hada da bindigogi kirar AK-47 sannan suka fara harbe-harbe kai tsaye.

‘Yan ta’addan sun yi garkuwa da mutane shida ciki har da wata mai ciki.

Majiyar ta kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun bukaci mutanen kauyen da su biya diyyar Naira 20,000 kowannensu nan da kwanaki bakwai masu zuwa ko kuma su fuskanci fushinsu.