An ci tarar Firaiministan Birtaniya saboda bai daura bel din mota ba

0
119

An ci tarar Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak saboda bai sa bel din motarsa ba, lokacin da yake daukar bidiyo a wayarsa.

‘Yan Sandan Lancashire sun ce sun yanke wa mutumin dan shekara 42 hukunci a birnin Landan tare da sharadi biyan tara cikin Æ™ayyadajjen lokaci.

Sun ce Mista Sunak “ya amince da chew ya yi kuskure kuma ya nemi afuwa”, ya kara da cewa zai biya tarar da aka ci shi.

Akan kama fasinjoji da suka gaza sanya bel dinsu lokacin da suke tuki, in kuma aka kama su akan ci su tara har fan 100. Kuma idan aka je kotu kudin kan iya kai wa fan 500.

An nadi bidiyon ne wanda aka wallafa a shafin Mista Sunak na Instagram domin sanar da matakin gwamnati na baya-bayan nan kan kashe-kashen kudinta.

Wannan ne karo na biyu da ake cin Mista Sunak tara yana rike da wani mukami.

A watan Afrilun da ya gabata, an ci shi tara tare da Boris Johson saboda karya dokar kulle a lokacin korona – sakamakon halartar wani biki a watan Yunin 2020.

Hukuncin tarar na laifin karya doka ne, wanda yake nufin dole a biya tarar cikin kwanaki 28 ko kuma a ɗaukaka ƙara.

Idan mutum ya zaÉ“i É—aukaka Æ™ara kan biyan tarar, ‘yan sandan za su sake bibiyar laifin sannan su yanke hukunci kan ko su janye tarar ko kuma sukai maganar kotu.

Jam’iyyar Demokrat tace “A matsayinsa na Firaminista na biyu da ke kan aiki da aka ci tara, wannan na nufin shi ma baya girmama doka kamar Boris Johson”.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here