Kocin tawagar ‘yan wasan tawagar Argentina, Lionel Scaloni ya ce dan wasa Lionel Messi ya sha gaban Diego Maradona a matakin fitatcen dan wasan kwallon kafa na duniya.
Scaloni ya ce idan an bani zabi a tsakaninsu Messi zan zaba, domin yana da wasu abubuwa na musamman a tare da shi sabpda shi ne fitatcen dan kwallo a duniya, koda yake Maradona ma ya yi fice kamar yadda Scaloni ya yi hira da gidan radiyon Cope a Argentina ranar Talata.
Mutane a Argentina sun fi kaunar Maradona fiye da Messi, sai dai watakila a samu sauyi nan gaba, bayan da dan wasan Paris St Germain ya ja ragama da Argentina ta lashe kofin duniya a Katar.
A watan jiya Argentina ta dauki kofin duniya na uku jumulla, kuma na farko tun bayan da Maradona yaja ragamar kasar ta lashe a shekarar 1986 sai dai a shekara ta 2014 taje wasan karshe inda tayi rashin nasara a hannun kasar Jamus.
Scaloni ya ce ya samu damar magana da Messi a lokacin da aka nada shi kociyan Argentina a 2018, inda ya rarrashi dan wasan PSG bayan da kasar ta kasa kai bante a gasar kofin duniya a Rasha.