Auren HIV: Ya aure ta shekara 2 bai sadu da ita ba

0
116

FAUZIYA D SULAIMAN ✍️

Idan ba ku manta ba a kwanakin baya ina yin posting na hada aure musamman masu fama da larura mai karya garkuwar jiki (HIV).

A cikin irin wannan masu larurar wata baiwar Allah ta ce min tana son yin aure, mijinta da iyayanta sun rasu kuma ba ta son cutar da kowa don haka na samo mata mai irin larurarta ta aura saboda ta gaji da zama haka ta samu mai tallafa mata.

 

Na zo nan social media na yi posting da kamanninta da yadda ta ke da me son auranta me irin larurarta, nan da nan Manema suka yi ta tura bukatarsu, duk Wanda ya tura hotonsa da bayaninsa sai na tura mata, har Allah ya sa suka daidaita da daya daga cikinsu, kasancewar ya ce shima yana da (HIV) ba su yi maganar gwaji ba, ba a fi wata da haduwar su ba aka daura aure, bayan sati biyu da auran ta tare.

 

Sai dai abun mamakin amarya ta tare tsahon sati guda ba ango, domin shi ba Dan garin Kano ba ne kasuwanci ne ke kawo shi don haka ya ce ta zauna anan sauran iyalinsa suna can garinsu, sai dai ya fake da mahaifiyarsa ce ta rasu shi ya sa bai zo ba.

 

Lokacin da ya zo bayan wani satin bai kula amarya ba tsahon kwanaki, shi da kansa ya ga rashin dacewar hakan, Don haka ya ce mata ta yi hakuri yana da larurar auratayya amma yana neman magani, ta ce ba komai Allah ta ba shi lafiya.

 

Tun daga wannan lokacin duk inda ta ji mai magani sai ta sanar da shi, wani lolaci idan ya tafi sai ya yi wata bata gan shi ba, sai dai ya aiko mata da Dubu Goma kudin abinci da na komai, har ya koma yana bata Dubu Biyar a wata guda, ta kira ni tana min complain na ce ta yi hakuri ta nemi abun yi.

 

A haka har aka kwashe shekara babu wani abu da ya shiga tsakaninsu, sai maganar biyan haya ta zagayo da kyar aka samu ya biya, idan ya wulla ya tafi sai ta gan shi, haka wani lokacin za ta zauna ba abinci, da ta sanar da ni halin da ake ciki na ce idan ba zai gyara ba su rabu kawai, sai ta ce tana tsoron ina za ta zauna tunda iyayanta sun rasu, kuma tana son samun ladan auran duk da har yanzu bai samu lafiya ba, tsahon shekaru biyu tana wannan halin watarana ba abinci balle sauran kayan bukatun rayuwa.

 

Garin ya aka yi ta jiyo labarin iyalinsa da yadda suke haihuwa, sai ta titsiye shi da garin yaya aka yi haka, sai Gogan ya ce zai gaya mata gaskiya shifa bashi da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV)

 

Mamaki da tashin hankali ya kamata domin tsahon lokacinnan tana ta yakin nemar masa magani da ganin ta samu ladan aure ashe lafiyarsa kalau bai da larura irin tata.

 

Cikin kuka ta ce masa ya san bai da wannan larurar mai ya sa ya aureta tsahon shekaru biyu yana wahalar da ita, sai mutumin nan ya yi shuru bai ce mata komai ba, tun cikin azumi da ya tafi har yanzu bai dawo ba, da sallah ma sai da na taimaka mata da wani abu, kuma ta-yi tayi ya saketa har yanzu ya ki sakinta kuma ya ki zuwa.

 

Abun tambayar anan me ya sa mutumin nan ya auri matarnan bayan yasan ba shi da irin larurarta? Dalilin da ya sa na daina tura matan da ke son su yi aure saboda mazan suna zaton masu kudi ne idan sun ji ba su da kudi sai su fasa, shin ko shima yana zaton tana da kudi ne shi ya sa ya aureta? Me ya sa ta ke ta rokon ya saketa ya ki sakinta bayan ba ya iya ciyar da ita, kuma lafiyarsa kalau, mugunta ce ko son zuciya?

 

To wannan amsar dai shi kadai ya santa, amma wallahi Allah ba zai bar shi akan wannan zaluncin da ya yiwa wannan baiwar Allah tsahon shekaru biyu da wani abu ba.

 

Abu na karshe na san yana following duk fejikana, idan har bai saki baiwar Allah nan ba, wallahi ni Fauziyya D. Sulaiman zan dauki matakin shari’a a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here